Kame-kamen masu shari′a a Najeriya | Siyasa | DW | 10.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kame-kamen masu shari'a a Najeriya

A Najeriya kame wasu alkalan da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi bisa zargin cin hanci da rashawa ya sake bankado badakalar da ake kullawa a fannin.

Wannan ne dai karon farko a shekaru masu yawa da aka kai ga kame alkalai har da na kotun koli bisa zargin cin hanci da rashawa a Najeriyar a wani mataki na yi wa wannan muhimmin sashi wankan tsarki da lalacewar al'amura.

Tuni dai kame alkalan ya sanya kungiyar lauyoyin Najeriyar barazanar lauyoyi su janye daga kotuna. Sai dai a bangaren masu sharhi na ganin akwai  dalilai masu karfi na zargin cin hancin.

Nigeria Gerichtshof in Abuja (DW/U. Musa)

Wuraren neman adalci sun zama dandalin cuwa-cuwa a Najeriya

Matsalar zargin katutun da cin hanci da rashawa ya yi wa sashin na shari'a a Najeriya, ya sanya daga  alkalai na kotun koli zuwa na kasa da kasa duka kanwar ta nemi zama ja jir.

Tuni  ra'ayoyi suka sha bamban a kan wannan mataki. A yayin da wannan batu ya jefa jamiyyun APC mai mulki da PDP ta ‘yan adawa cikin sabon cacar baki a kan kame alkalan da PDP ke cewa kokarin cin zarafi ne, za'a dai a sa ido a ga ko komar jami'an tsaron za ta sake cafko wasu da ake zargi kafin gurfanar da wandanda aka kama a gaban shari'a domin a yi musu abin da sukan yi wa wasu a baya.

 

Sauti da bidiyo akan labarin