Kamaru ta yi nasarar kubutar da mutanenta | Labarai | DW | 19.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta yi nasarar kubutar da mutanenta

Sojojin kasar ne suka kwato mutane 24 daga cikin 80 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a kan iyakar kasar da makwabciyar ta Najeriya a jiya Lahadi.

Harin da Boko Haram din ta kaddamar kan kauyen Mabass, ya kasance hari mafi girma da ya kai ga garkuwa da jama'a a kasar, inda a ciki aka yi garkuwa da kananan yara.

Kamar dai yadda kakakin ma'aikatar tsaron kasar ta Kamaru, Kanal Didier Badjeck ya shaida wa manma labarai, sojojin na Kamaru sun yi nasarar kwato 'yan kasar ta su ne, sakamakon matsawa 'yan bindigan da ke kan hanyar su ta komawa cikin tungar su da ke a Najeriya.

Kungiyar Boko Haram dai ta kashe dubban mutane tare da garkuwa da daruruwan wasu a arewacin Najeriya.

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa

edita: Usman Shehu Usman