1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta mayar da 'yan gudun hijira Najeriya da karfi

Uwais Abubakar Idris
September 27, 2017

Kungiyar kare hakin jama'a da Human Rights Watch ta fitar da wani rahoto da ta zargi kasar Kamaru da talasta ‘yan gudun hijira na Najeriya dubu-dari zuwa Najeriya.

https://p.dw.com/p/2koSi
Nigeria UN Camp in Maiduguri
Hoto: imago/epd/A. Staeritz

Rahoton da kungiyar ta kare hakin jama'a ta Human Rights Watch ta fitar ya zargi  sojojin kasar Kamaru da azabtar da cin zarafin ‘yan gudun hijira ‘yan Najeriya da duban masu neman mafaka da yakin Boko Haram ya  tilasta masu tsallakawa zuwa Kamaru amma maimakon samun sa'ida sai suka sake fadawa cikin wani bala'in da suka baro.

Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wannan rahoto da aka yi wa take da sun tursasamu cikin motocin tirela tamkar dabbobi ya nuna damuwar yadda  sojojin Kamaru suka ci zarafin mata da ke neman mafaka ta hanyar yin lalata da su tare da hana su samun kariya daga hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya. Mr Gerry Simpson shi ne jami'n kungiyar mai kula da Najeriya da Kamaru da ya gabatar da rahoton.

Abin da yafi daga hankali shi ne yadda Human Rights ta gano yadda gwamnatin Najeriya ta taimaka tasa keyar ‘yan kasarta inda a watan Yuni ta aika da motocin sojoji da suka kwaso mutanen, da bisa tilas aka tusasa masu komawa wuraren da babu kwanciyar hankali inda a tuni an kashe mutane 20 daga cikin wani harin da aka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na  garin Banki. Rev Joseph John Hayab shi ne shugaban cibiyar wazar da zaman lafiya na cikin wadanda suka nazarci rahoton.

Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Harnik

Kungiyar kare hakin jama'a ta Human Rights Watch ta ce za ta daga wannan batu a wajen taron hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin duniya da za a yi, domin ta yi kokarin jin ta bakin mahukuntan kasar Kamaru amma abin yaci tura. Kasar Kamaru dai ta shiga cikin jerin kasashe hudu da suka yi kaurin suna wajen tilasata ‘yan gudun hijira su bar kasarta.