Kamaru ta bude gasar AFCON da kafar dama | Labarai | DW | 09.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta bude gasar AFCON da kafar dama

2-1: Wannan shi ne sakamakon nasarar da Kamaru ta samu a kan Burkina Faso a wasan farko na AFCON da shugaban FIFA Gianni Infantino da Shugaba Paul Biya na Kamaru suka halartai a filin wasa mai daukar mutum 60,000.

Kasar Kamaru mai masaukin baki a gasar cin kofin Afirka ta AFCON da aka bude a yammacin wannan Lahadi ta fara gasar da kafar dama. A fafatawar da suka yi tsakaninsu da Burkina Faso, Kamarun ta yi nasarar zura kwalla 2 a raga, a yayin da Burkina Faso ta yi kokarin zura wa kamaru kwallo guda 1. 

Tun da farko sai da aka dauki lokaci ana bikin bude gasar da ke zama mafi daukaka a harkar kwallon kafa a nahiyar Afirka kafin a amincewa kasashen biyu da ke a rukunin A su kece raini.

An jima kadan da misalin karfe 8pm agogon Najeriya kasar Cape Verde da Habasha da su ma ke cikin rukunin A za su barje gumi a tsakaninsu a wannan gasa ta AFCON.