Kamaru: Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane 1,500
November 16, 2016Kungiyar sa idon kan harkokin tsaron ta International Crisis Group a Kamaru ta ce ko da yake mahukuntan na Kamaru suna samun nasara a yakin da suke yi da Boko Haram musamman a lardin Arewa mai nisa, har yanzu ba'a kawar da matsalolin da ke zama taki ga rikicin ba. Wadannan matsaloli a cewar Hans De Marie Heungoup na kungiyar ta ICG a Kamaru sun hada da matsaloli na talauci abin da yace kungiyar ta Boko Haram ke amfani da wannan dama wajen jan ra'ayin matasa ta hanyar yi musu dan hasafi:
"Abin da yake a zahiri dai shi ne cewa kantar talauci a arewacin Kamaru ya bada damar shigar 'yan Boko Haram tare da daukar mayaka a tsakanin al'umma musamman a yankunan kan iyaka kamar Fotokol da Kolo fata da sauran yankuna na kan iyakar."
Ya ce idan aka yi lakari, za'a ga cewa Boko Haram, sannu a hankali ta shiga kasar Kamaru daga watan janairu na shekarar 2014 inda ta ke yin barazana ga hukumomi har ma da gargadin kasar a kan kada ta sa kanta a rikicin da kungiyar ke yi da Najeriya. Sai dai kuma bayan da kasar ta Kamaru ta zafafa kai farmaki kan kungiyar ta Boko Haram, kungiyar ta ce ta ja daga kuma ta shiga yaki da kamarun ta hanyar kai hare hare ba kakkautawa.