Kamaru na kula da ′yan gudun hijirar Taraba | Siyasa | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamaru na kula da 'yan gudun hijirar Taraba

Kimanin mutane dubu bakwai da shanu fiye da dubu biyu suka tsallaka daga Najeriya zuwa kasar Kamaru, saboda rikicin Jihar Taraba. Lamarin da ya janyo matsalolin ayyukan jin kai a bangaren kasar Kamaru.

Jami'an Kamaru da ma'aikatan agaji na kula da 'yan gudun hijira da ke fama da rashin lafiya a wata cibiya ta Kiristoci mabiya darikar Katolika. 'Yan gudun hijiran dai na fama da yunwa da kishirwa bayan doguwar tafiya da kafa daga Jihar Taraba zuwa kasar Kamaru. Bello Dewa Oumar dan shekaru 53 yana cikin wadanda suka tsere daga garin Bamga na Karamar hukumar Gembu inda aka samu hatsaniya tsakanin kabilar Manbila da Fulani makiyaya.

" 'Yan Mambila suna neman ganin bayan Fulani baki daya a yankin, inda suke kashe kowa da shanu. Waje daya da ya rage kawai a Mambila da ake iya shiga shi ne Mbamga, ni ma dakyar na tsallake. Galibin tsageru 'yan Mambila suna fakon Fulani masu neman tserewa zuwa kasar Kamaru. Dole na bi ta cikin dokar jeji"

Kimanin mutane dubu bakwai da suka tsere zuwa Kamaru, sun shiga da shanu fiye da dubu biyu. Sai dai a cewar Bello Dewa Oumar barayi sun kwace mafiya yawan shanun.

Mata da yara sun kasance galibin wadanda suke tsallaka Kamaru neman gudun hijira, Jean Marie Kou na cikin ma'aikatan lafiya na cibiyar Kiristoci mabiya darikar Katolika.

"Mun fara kula da su da abin da cibiyar take da shi, saboda mutanen ba su da komai. Mun yi iya bakin kokar, amma babu kayayyakin da muke bukata sossai. Idan gwamnati ba ta kawo daukin magunguna ko kuma biyan kudaden maganin na 'yan gudun hijira ba, za mu shiga babbar matsala da ba za mu iya kula da 'yan kauyuka ba kamar yadda aka saba."

Yanzu akwai matsala tsakanin 'yan gudun hijira da kuma al'ummomin da suka karbe su, manoma sun koka da yadda shanu suka fara ta'adi ga amfanin gona. Amma gwamnatin Kamaru ta ba da umurnin baiwa 'yan gudun hijran mafaka a makarantu.

Jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, na da fiye da kabilu 80 inda wasu lokuta ake samun sabani tsakanin juna. Rahotanni sun nuna cewa a watan Mayu tsageru sun kai hari kan Fulani, wannan ya sa gwamnatin Najeriya ta ce rikicin baya da nasaba da addini amma zaman tankiya tsakanin makiyaya da manoma ke ruwa wutar rikicin.

Sauti da bidiyo akan labarin