1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru:Paul Biya na neman sulhu da 'yan aware

Abdourahamane Hassane
September 12, 2019

A karshen watan Satumba gwamnatin Kamaru za ta shirya tattaunawa da 'yan aware domin samun hanyoyin warware rikicin kasar da aka kwashe kusan shekaru uku ana yi, sai dai ba a da tabbas ko 'yan Ambazonia za su halara.

https://p.dw.com/p/3PTOK
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Lintao Zhang

Shugaban Kasar Kamaru Paul Piya ya kira babban taron neman sulhu a karshen watan Satumba domin samun masalha a game da yakin basasar da ake faman yin a kasarsa kusan shekaru uku tsakanin gwamnatin da 'yan aware na Ambazonia masu neman kafa kasarsu. Sai dai ba tabbas ko tattaunawar za ta yi nasara sakamakon yadda 'yan Ambazonia suka ce ba za su halarci taron ba saboda rikici ne tsakaninn kasashe biyu don haka Kamaru ba ta da hurumin shiga tsakani.