1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Bamenda ya yi illa ga kiwon lafiya

September 3, 2019

A Kamaru harakokin kiwon lafiya sun fuskanci babban komabaya a Jihar Bamenda, a sakamakon rikicin da ake fama da shi a yankin inda aka kone gidajen asibiti da dama a yayin da wasu da dama suka rufe kofofinsu.

https://p.dw.com/p/3Ox1m
Symbolbild Apotheke Äquatorialguinea
Mun yi amfani da tsohon hoto neHoto: imago/imagebroker

A kasar Kamaru harakokin kiwon lafiya sun fuskanci babban komabaya a Jihohin Bamenda da Bue na yankin masu amfani da Turancin Ingilishi, a sakamakon rikicin da ake fama da shi a yankin inda aka kone gidajen asibiti da dama. Lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen likitan rufe kofofinsu. Abin da kuma ya haifar da matsalar rashin kula da lafiyar al'umma a wannan yanki.


Wannan rufe wasu asibitoci da aka yi a Bamenda ya haifar da matsalar karuwar marasa lafiya a sauran asibitoci kadan da ke bude, inda za ka tarar da jerin gwanon mutane masu son ganin likita a layi, duk da cewa babu tabbacin za su gane shi, wanda haka ya sa wasu ke karya domin gani likita. Sai dai a cewar Baldwin Chi, jami'in kiwon lafiya na majami'ar Baptist ta kasar Kamaru yawan majinyata a asibitoci na karuwa ne a kullum da kashi 30% cikin dari:

"Mun ga gagarumar nasara a duba marasa lafiya da muke yi, musamman da kayayyakin aiki na kulawa da yara kanana da iyaye mata, a cibiyoyin kula da lafiya kamar na HIV. Mun samu karuwar marasa lafiya da kusan kashi 30% cikin dari."

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Baldwin Chi ya kara da cewar an kawo karin daruruwan ma'aikatan kiwon lafiya daga cibiyar kula da lafiya ta CBC domin taimaka wa dumbin marasa lafiyan asibitin:


"Irin wannan halin da ake ciki na tururuwan marasa lafiya ba sabon abu ba ne a bangaren ma'aikatanmu, ganin cewar rikicin ya jagoranci rufe cibiyoyin kiwon lafiyan na karkara da yankuna masu yawa, kasancewar suna karkashin manyan asibitoci. Hakan ne ya sa aka sake tura jami'an cibiyoyin da ke bude a garuruwa kamar nan Bamenda. An turasu sassan da ke da cinkoson jama'a."

Samun damar ganin likita ya zama babbar nasara ga marasa lafiya saboda irin layin da ake yi. Sonia Kum ta kasance daya daga cikin majinyata da ke fama da cutar Suga, ta saba ganin likitanta a kowane wata, batu da a yanzu sai ta yi gwaggwarmayar samun hakan:

" Mun tsere daga Wum kuma yanzu muna samun mafaka wajen dan uwana a nan Bamenda. Ina zuwa ganin likita a kowane wata. Idan da ina Wum, da a yanzu haka na ga likita, amma a nan akwai dogon layi, na san zan sha wahala kafin na gan shi, duk da haka zan samu ganinsa. Kowa ya tsere daga garin Wum har da lilitoci" 

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Domin shawo kan matsalar a yanzu haka, tawagar jami'an kiwon lafiya na gundumar, sun kaddamar da gwajin wasu cututtuka kyauta ga jama'a kamar Hepatitis B da C. Kinsly Che Soh, shi ne ke wakiltar yankin Arewa maso yammaci, wanda ya bayyana irin wahalar da mutane suka shiga saboda barkewar rikicin. A cewarsa mutane da dama ba su da sukunin samun kulawa da lafiyarsu. Dangane da haka ne aka tsara fadada batun yin gwajin zuwa wasu yankunan.

A daidai lokacin da rikicin yankin Kamaru masu magana da harshen Turancin Ingilishi ke kara kamari, harkokin kula da lafiya na ci gaba da zama babban kalubale, kasancewar asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya na ci gaba da rufewa. Su ma likitocin agaji na kasa da kasa da ke kasar ba za su shawo kan matsalar ba, kasancewar a manyan garuruwa kawai suke aiki.