Kamaru: Harin bam a wata kasuwa | Labarai | DW | 19.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru: Harin bam a wata kasuwa

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadi na rayukan mutane da dama a Arewacin na Kamaru, harin da Boko Haram ta saba Kai irinsa a kasar.

Kamerun Anschlag in Maroua

Yankin da aka kai harin bam a Arewacin Kamaru

Wasu tagwayen hare-haren bama-bamai a wata kasuwa a lardin Meme da ke a Arewacin Kamaru ya yi sanadi na rayukan mutane 19, yayin da wasu 50 suka samu raunika kamar yadda mazauna yankin suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Wannan dai shi ne hari na baya-bayan nan da ya yi sanadi na rayukan mutane da dama a Arewacin na Kamaru da ke ganin yawaitar ayyukan ta'addanci daga kungiyar Boko Haram mai sansani a Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin wannan kai hari da aka saba ganin kungiyar ta Boko Haram na kaishi.