1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar rikicin siyasa a Kamaru bayan zabe

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
October 9, 2018

'Yan siyasa a Kamaru, na tayar da jijiyoyin wuya dangane da ikikarin da guda daga cikin 'yan takara Maurice Kamto ya yi na lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a karshen mako.

https://p.dw.com/p/36F8X
Kamerunesischen Botschaft in Tschad
Hoto: DW/B.Dariustone

Magoya bayan dan takara Maurice Kamto ba su yi mamakin matsayin gwanin nasu na bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa ba, saboda tun lokacin da aka fara kidaya kuri'u suka yi amannar cewar zai lashe zaben da aka gudanar ranar bakwai ga watan Oktaban da muke ciki. Sai dai a hannu guda, al'ummar kasar na nuna fargabar sake fadawa rikicin siyasa irin wanda kasar ta taba samu kanta ciki a lokacin da ta koma kan tafarkin dimukuradiyya.

Nesanta kai daga riga malam Masallaci

A hannu guda kuma, wasu daga cikin 'yan takarar adawar sun nesanta kansu da ayyana nasara ta gaban kai da Maurice Kamto ya yi a zaben shugaban kasar da ya gudana, tare da bayyana matakin nasa da yunkurin kawo rudani. Su ma kusoshin jam'iyyar RDPC ko CPDM da ke mulki sun nuna bacin ransu dangane da take dokar zabe da daya daga cikin 'yan takara ya yi, inda Hervé Emmanuel Nkom da ke zaman guda daga cikin jami'an yakin neman zaben Biya ya nuna wajibcin gurfanar da Maurice Kamto gaban kuliya.

Kamerun, Maurice Kamto
Hoto: AFP/Getty Images

Faragabar rikicin bayan zabe

Wannan fargaba da 'yan siyasar Kamaru ke nunawa dai, ba ta rasa nasaba da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben 1992 shekaru 26 da suka gabata, inda jam'iyyar SDF ta zargi Paul Biya da murde zaben. Harkokin yau da kullum sun shafe watanni suna tafiyar hawainiya a wancan lkaci bayan da madugun 'yan adawa John Fru Ndi ya yi kira da gudanar da yajin aikin gama gari, lamarin da ya jefa Kamaru cikin matsin tattalin arziki. Theophile Kouamouo da ke zama dan jarida da ke sharhi kan al'amuran siyasa a Kamaru ya ce a wannan karon ma za a iya fadawa cikin sabon rikicin bayan zabe. Tun lokacin da aka kammala kidaya kuri'u ne wasu 'yan Kamaru suka fara wallafa sakamakon da aka samu a runfunansu. Sai dai ba za a san wanda ya lashe zaben ba sai nan da makonni biyu lokacin da shugaban kotun tsarin mulki zai bayyana sakamako na dindindin.

.