1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Boko Haram ta halaka mutun 18 a Kamaru

Gazali Abdou Tasawa
August 3, 2020

Mahukuntan kasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 18 a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai a sansanin 'yan gudun hijira na yankin Arewa mai nisa na kasar a karshen mako.

https://p.dw.com/p/3gIwX
Kamerun Amchide Armee Soldaten Anti Boko Haram 11/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa mutane akalla 18 ne suka halaka a cikin wani hari da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kai shi a daren Asabar washe garin Lahadi a sansanin 'yan gudun hijira na Nguetchewe na karamar hukumar Mayo-Moskota a yankin Arewa mai nisa na kasar ta Kamaru sansanin da ga al'ada jama'ar yankin ke zuwa neman mafaka a duk lokacin da kungiyar Boko haram ta kai hari.

 Wasu shaidun gani da ido a yankin sun ce akwai fargabar karuwar mutuwa a nan gaba domin da dama daga cikin wadanda suka jikkata da aka kwatar da su a asibiti sun rasa wasu sassa na jikinsu. A makon da ya gabata sojojin gwamnatin kasar ta Kamaru sun halaka mayakan na Boko Haram guda biyar a wannan yanki.