1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Biya ya fara sabon wa'adin mulki

Zulaiha Abubakar
November 6, 2018

An rantsar da shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru mai shekaru 85 a daidai lokacin da rikici ya ke kara kamari a yankin masu magana da Turancin Ingilishi.

https://p.dw.com/p/37jwD
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Warnand

Da ya ke gabatar da jawabi a yayin shagalin bikin rantsuwar da kakakin majalisar Dokokin kasar Cavaye Yeguie Djibril ya jagoranta, Shugaba Biya ya jaddada aniyarsa ta maido da martabar kasar. Wannan dai shi ne wa'adin sa na bakwai a shugabancin kasar. Sama da mutane dubu 300 daga cikin al'ummar kasar ne ke zaune a dazuzuka cikin yunwa a halin yanzu sakamakon gujewa rikicin 'yan aware masu neman kafa kasar Ambazoniya daga cikin Kamarun.