1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen da ake fuskanta a manyan makarantun Najeriya

Abdullahi Tanko Bala SB
January 24, 2022

Ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin waiwaye kan harkokin ilimi a duniya inda aka duba kalubalen da Jami'oi ke fuskanta a Najeriya.

https://p.dw.com/p/460hT
77 | Najeriya taimakon dalibai da suka bar makaranta
Najeriya taimakon dalibaiHoto: DW

Jami'a babbar makaranta ce da ke bada Ilmi mai zurfi tare da horar da dalibai a fannoni da dama na rayuwa kuma jami'a ita ce take horar da shugabanni na gaba da kaifafa fasaha don cigaban kasa da al'umma baki daya.

An yi itifakin cewa Ilmi shi ne jigon habaka kyakkyawar zamantakewa da tattalin arziki da siyasa da raya al'adu. A mahangar masana Ilmi ana iya duba gudanar da Jami'a ta fuskoki guda biyu a ciki da waje. A waje gwamnatin tarayya da ke iko da jami'oi bisa sa idon hukumar kula da jami'oi ta kasa NUC da gwamnatin ta dora wa alhakin yin hakan sai kuma mataki na cikin gida na tafiyar da jami'oin karkashin shugabancin Vice Chancellor na gudanar da harkokin yau da kullum na jami'ar.

Bincike ya nuna jami'oi da dama a Najeriya na fama da kalubale masu yawa da suka hada da rashin isasun kudade da lalacewar kayayyakin koyo da koyarwa da gine gine da kuma uwa uba rashin isasun malamai. To ko me ya sa matsalolin suka yiwa bangaren Ilmi katutu musamman na jami'a? Farfesa Yakubu Magaji Azare malami ne a jami'ar Bayero da ke Kano, wanda ya nuna muhimmancin ilin da Saboda a fage na Ilmi dan Adam ake ginawa shi kuma dan Adam idan ya ginu shi ne yake gina al'umma.

Najeriya Abuja | Zanga-zanga| Neman samar da tsaro kan harkokin ilimi
Zanga-zanga kan neman gyara ilimiHoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Yawan dalibai a Jami'oin Najeriya ya kai matukar da ya fi yawan malaman da ake da su kamar yadda hukumar kula da jami'oi ta kasa NUC ta nunar kuma a cewar Dr Tukur Abdulkadir tsohon shugaban kungiyar malamai ta kasa ASUU reshen jami'ar jihar Kaduna abin da ya jawo hakan shine jama'a da dama basa sha'awar koyarwa saboda rashin albashi ingantaccen albashi  da zai karfafa su ga kuma matsalolin da har yanzu ba'a warware su ba

Wani batu da ke jawo kalubale ga ilmin jami'oi a Najeriya shi ne yawan yajin aikin malamai lamarin da daliban ke kokawa, sai dai sabanin tunanin daliban malaman na cewa in ba don yajin aikin ba da ma yanzu babu jami'oin, saboda yadda gwamnati ke ci gaba da rage kudin manyan makarantun kamar abin da ya faru da kananan makarantu.

Jami'oi mallakar gwamnati sun dogara ne kacokam akan gwamnati wajen samar musu kudade, kuma a duk shekara gwamnati na yin kasafin kudi tare da ware kaso ga jami'oi shin ina kudaden ke tafiya? Farfesa Andrew Haruna tsohon shugaban jami'ar Gashua a Najeriya ya yi tsokaci kan irin tarnaki kudi da ake fuskanta saboda ba kasafai gwamnatin take bayar da daukacin kudin da ake bukata ba. 

Yayin da wadannan matsaloli suka yi wa jami'oin dabaibaiyi ko ina mafita? Dr Tukur Abdulkadir tsohon shugaban kungiyar malamai ta ASUU ya yi bayani da cewa dole sai a tunkari matsalolin kafin fita daga yayin da ake ciki. Shi kuwa Farfesa Andrew Haruna tsohon shugaban jami'ar Gashua yace dole ne a hada karfi da karfe don ceto Jami'oin daga durkushewa