Kafa gwamnatin Palasdinawa | Labarai | DW | 11.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kafa gwamnatin Palasdinawa

P/M Palasdinawa Ismaila Haniya yace zai kammala kafa gwamnatin hadin kann kasa a ranar Alhamis mai zuwa, kana a ranar Asabar kuma ya bukaci amincewar majalisar dokoki. Matakin kafa gwamnatin ta biyo bayan cimma yarjejeniyar da aka yi ne a saudiya a tsakanin Ismaila Haniya da kuma shugaba Mahmoud Abbas. A waje daya kuma wasu yan bindiga dadi daga bangaren Fatah sun bude wuta a kan jerin gwanon motocin wani Minista na Hamas a gabar yamma da kogin Jordan. Wannan shi ne hari na farko mafi muni tun bayan da bangarorin biyu suka fara tattaunawar kafa gwamnatin hadin gambiza. A yau ne kuma ake sa ran shugaba Mahmoud Abbas zai gana da P/M Israila Ehud Olmert.