Kaduna: Matasa masu sana′ar sayar da kwadi | Himma dai Matasa | DW | 11.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kaduna: Matasa masu sana'ar sayar da kwadi

A wani mataki na yaki da zaman kashe wando tsakanin matasan Kaduna wasu gungun marasa aiki na yin sana’ar kamun kwadi daga rafin Kadunan wanda suke sayar da su.

Matasa masu yawa ne a wata unguwar ta Kaduna da ake kira da sunan Gwari suka yi watsi da wasu kananan sana’o’in hannu da suke yi domin rungumar sana’ar kamun kwadi da suke samun makudan kudade a kowace rana. Sana’ar dai a cewar shugaban matasan Felix Peter na bunkasa a arewacin Nigeria sakamakon yadda wasu kabilun ke bukatar naman kwado da kuma yadda ake magani da bangaren jikinsa.
 

Sauti da bidiyo akan labarin