1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin soja ya yi hatsari a Senegal

March 16, 2018

Akalla mutane takwas sun mutu yayin da wasu 12 kuwa suka jikkata a wani hatsarin jirgin sama mai saukar angulu a sashen yammacin kasar Senegal.

https://p.dw.com/p/2uQb3
Russland Sotschi Flugzeugabsturz - Rettungsoperation
Hoto: picture-alliance/Sputnik/N. Zotina

Rahotannin da ke fitowa daga Dakar babban birnin kasar Senegal, na cewa akalla mutane takwas sun mutu yayin da wasu 12 kuwa suka jikkata a wani hatsarin jirgin sama mai saukar angulu a sashen yammacin kasar. Kamar dai yadda jami'an lafiya ke cewa, ana can ana kulawa da sauran wadanda suka rayun, sai dai suna cikin mummunar yanayi sakamakon irin raunukan da suka samu a hatsarin, a cewar shugaban asibitin garin Kaolack, Saliou Tall.

Jirgin mai saukar angulu mai lamba Mi-17, jirgi ne na zirga-zirgar sojoji, kuma ya fuskanci matsala ne yayin da yake sararin samaniyar kauyen Missirah da ke kusa da iyaka da kasar Gambiya. Ba a dai kaiga bayar da cikakkun bayanai kan musabbabin hatsarin ba, a hukumance, sai dai sojoji sun ce suna gudanar da bincike.