Jirgin fasinja a Rasha ya yi hadari | Labarai | DW | 11.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin fasinja a Rasha ya yi hadari

Jirgin dai dauke da fasinja ya bace wa na'urar da ke nazarin jirage a samaniya jim kadan bayan tashi daga filin jiragen sama na Domodedov kan hanyarsa ta zuwa birnin Orsk.

Rahotanni da ke shigowa daga Moscow na cewar wani jirgin daukar fasinja na Saratov Airlines a Rasha dauke da kimanin mutane 71 ya fado a kusa da birnin Mascow kamar yadda kamfanin dillancin labarai TASS ya ba da rahoton da ya danganta daga jami'an tsaro na farin kaya. Jirgin dai dauke da fasinja ya bace wa na'urar da ke nazarin jirage a samaniya jim kadan bayan tashin jirgin daga filin jiragen sama na Domodedov kan hanyarsa ta zuwa birnin Orsk. Akwai dai fargabar cewa fasinjan da ke cikin jirgin duka sun mutu.