Jirgi mai saukar angulu ya fadi kusa da Yola | Labarai | DW | 10.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgi mai saukar angulu ya fadi kusa da Yola

A wannan Litinin wani jirgin sama mai saukar angulu dauke da wasu Turawa, ya fadi kusa da birnin Yola, helkwatar Jihar Adamawa a Tarayyar Najeriya.

Wani jirgin sama mai saukar angulu, dauke da wasu Turawa ya fadi a kusa da birnin Yola, helkwatar Jihar Adamawa. Kawo yanzu babu wani tabbacin sanadiyyar faduwar jirgin, kuma hukumomi ba su yi bayani kan lamarin ba.

Amma wani jami'in hukumar yaki da fasa kwabri da bai so a ambaci sunansa ba da ke bakin aiki a dab da inda jirgin ya fadi, ya shaida wa wakilinmu da ke Yola cewa tabbas jirgin na dauke da Turawa 12 kuma hudu daga ciki sun ji rauni. Sai dai kawai binciken hukumomi ne zai tabbatar da dalilin faduwar wannan jirgi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman