Jiragen yakin Faransa sun kai hari kan IS | Labarai | DW | 16.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen yakin Faransa sun kai hari kan IS

A wannan Lahadi da ta gabata jiragen saman yakin Faransa sun kaddamar da hare-haren bama-bamai kan cibiyar kungiyar IS da ke a birnin Raqqa na Siriya wacce ta dauki alhakin hare-haren birnin Paris.

Jiragen yakin kasar Faransa sun kaddamar a jiya Lahadi da wasu jerin hare-haren bama-bamai a kan cibiyar kungiyar IS da ke a birnin Raqqa na kasar Siriya a wani mataki na mayar da martani ga kungiyar wacce ta dauki alhakin kai harre-haren birnin Paris na ranar Jumma'ar da ta gabata.

Gwamnatin kasar ta Faransa ta ce jiragen yakin sun jefa bama-bamai 20 a birnin na Raqqa inda suka lalata wasu ofisoshin dama da wata cibiyar horas da mayakan kungiyar.

Ministan tsaron kasar ta Faransa ya ce Jiragen yakin kasar 12 ne wadanda suka taso daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jodan suka kaddamar da hare-haren wadanda Faransar ta tsara kai su tare da goyan bayan sojojin Amirka.

Wannan dai shi ne karo na farko da Faransar ta kaddamar da hare-haren kan kungiyar ta IS ta hanyar amfani da wadannan kasashe na Larabawa.