Jiragen saman Isra´ila na ci-gaba da kai farmaki a Zirin Gaza | Labarai | DW | 26.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen saman Isra´ila na ci-gaba da kai farmaki a Zirin Gaza

Isra´ila na ci-gaba da kai hare hare ta sama akan Zirin Gaza. Harin wasu makamai masu linzami da Isra´ila ta kai da sanyin safiyar yau asabar sun afkawa sansanonin sojin sa kai da wani wurin bincike dake kusa da gidan FM Falasdinawa Isma´il Haniya. A wani samame da suka kai cikin dare sojojin Isra´ila sun sake kame wani minista dan Hamas dake cikin gwamnatin Falasdinawa. Dakarun Isra´ila suka yi awon gaba da ministan kasa Wafsi Qabha daga gidansa dake Yammacin Kogin Jordan. A kuma halin da ake ciki sojojin sa kai na Falasdinawa sun bawa Isra´ila wa´adin sa´o´i 48 da ta amince da wani shirin tsagaita wuta a Zirin Gaza. Wani wakilin shugaba Mahmud Abbas ya ce wannan yarjejeniya zata sabunta wani shirin tsagaita wuta da shugaban na Fatah da kuma FM Isra´ila Ehud Olmert suka kulla a cikin watan nuwamban bara. To sai dai sojojin sa kai sun musanta cewa ba su alkawarta wani shiri ba.