Jiragen sama na shan mai a wajen Najeriya | Labarai | DW | 13.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen sama na shan mai a wajen Najeriya

Kamfanoni da ke samar da man jiragen a Najeriya irinsu Total da Sahara da ConocoPhillips, sun rubanya farashin mansu.

Flugzeug KLM

Jami'ai na jirgin KLM dai sun ce ba kasafai suke yin ahaka ba a Najeriya

Tsadar farashin man da jirgin sama ke amfani da shi ta sanya jiragen sama na kasashen waje da ke jigila zuwa Najeriya na zuwa wasu kasashe dan cika tankunan jiragensu kafin su shiga Najeriya ko idan sun fita dan kaucewa siyan man da tsada a kasar, lamarin da ke da nasaba da rashin kudaden waje da masu siyo man daga waje ke amfani da su dan siyo man ya wadata a kasar.

Kamfanoni da ke samar da man jiragen a Najeriya irinsu Total da Sahara da ConocoPhillips,sun rubanya farashin mansu kamar lita guda da ake siyarwa a kan Naira 220 a watan Agusta yanzu ta kai Naira 400 kamar yadda wani jami'i a kamfanin zirga-zirgar jiragen saman ya bayyana.

Wannan na zuwa ne dai a lokacin da wasu jiragen na kasashen waje suka tsaida jigilarsu zuwa Najeriya, yayin da wasu ma a cikin gida suka tsaida zirga-zirga.