1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana binciken hatsarin jirgin kasa a Indiya

June 5, 2023

Jiragen kasa sun dawo da zirga-zirga bayan hatsarin da ya yi sanadiyyar rayuka a Balasore babban birnin Odisha da ke kasar Indiya a ranar juma'ar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4SDHW
Indien | Wiederaufnahme des Bahnverkehrs nach Zugunglück von Balasore
Hoto: Adnan Abidi/REUTERS

Wannan hatsarin shi ne daya daga cikin manyan iftila'in da suka fadawa kasar a baya bayan nan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300 tare da jikkata daruruwan wasu. Tuni dai Jami'an tsaro suka kaddamar da bincike kan wannan iftila'in.

Ministan sufurin jiragen kasa Ashwnin Vaishnaw ya danganta hatsarin da samun matsalar lalacewar na'urar lantarki da jirgin ke amfani da shi.

Jami'an layin dogo da shaidu sun taru don gabatar da shaida ga wani binciken na kwanki biyu da suka gabata, karkashin jagorancin kwamishinan kula da lafiyar jiragen kasa a jihar West Bengal mai tazarar kilomita 120 daga wurin da hatsarin ya faru.