Jinkiri a ci-gaban tattalin arzikin China | Labarai | DW | 19.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jinkiri a ci-gaban tattalin arzikin China

Hukumomi a kasar China sun ce bunkasar tattalin arzikin kasar a wannan tsukin shi ne mafi jinkiri da aka fuskanta a cikin shekaru shidan da suka gabata.

Wannan dai na kunshe ne cikin wasu sabbin alkaluma da China ta fitar dai dai lokacin da take fadi-tashi wajen ganin tattalin arzikin ya samu tagomashi.

Gabannin kai wa ga wannan gaba dai, China ta dauki matakai na bunkasa tattalin arzikinta da ma zaftare kudaden ruwa da aka yi a lokuta da dama a cikin kasar.

To sai dai duk da wannan yanayi da ake ciki, masu sanya idanu kan yadda tattalin arzikin kasar ta China ke tafiya na cewar alkaluman fa sun yi kyau matuka domin kuwa ba su yi zaton za ma a kai ga haka ba. Tattalin arzikin China dai shi ne na biyu mafi karfi a duniya.