Jihar Imo ta nisanta kanta da rijista wa ′yan arewa | Siyasa | DW | 17.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jihar Imo ta nisanta kanta da rijista wa 'yan arewa

Gwamnan Jahar Imo Rochas Okorocha da ke kudu maso gabashin Najeriya ya musanta hannu kan yi wa 'yan arewacin kasar rijista

Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo ya ce ba yi da hannu bisa bullo da katin rijista ga 'yan arewacin Najeriya da ke jihar suna kasuwanci.

Gwamnan Okorocha ya ce gwamnatinsa ba ta da hannu a cikin shirin, kuma babu wani umurnin yin rijista ga wani, saboda yana sane da cewa haka ya saba dokokin kasa. Ya kara da cewa zai yi kyau masu zargin gwamnatin su fara gudanar da bincike na sanin abin da yake faruwa.

Gwamnan jihar ta Imo ya Rochas Okorocha ya kuma yi bayani bisa harkokin siyasa na kasar, inda ya nunar da cewa rashin hadin kai ke zama babbar ga jam'iyyar adawa ta APC. Gwamnan ya yi kalaman ya yi hira da wakilin DW na yankin Niger Delta Muhammad Bello.

Alhaji Faisal Lawal da ke zaman mai bai wa Gwamnan na Imo shawara kan Alammurran 'yan Arewa ya ce dama ba hannun gwamnatin Imo cikin tsarin na yin rijista. Kuma shugabannin al'umar 'yan Arewa ke gudanar da shirin bisa radin kai.

Mawallafi: Muhammad Bello
Edita: Suleiman Babayo