Jega ya ce ba zai yi murabus ba | BATUTUWA | DW | 19.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Jega ya ce ba zai yi murabus ba

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya yi watsi da kiraye-kiraye da wasu ke yi na ya sauka daga mukaminsa kafin zaben shugaban kasa da ke tafe.

Nigeria Wahlkommision verschiebt Wahltermin Attahiru Jega

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega

Farfesa Jega ya ce saukarsa daga mukaminsa a wannan gaba ba za ta haifawa Najeriya da mai idanu ba, don haka yanzu ya dukufa ne wajen yin aikinsa yadda ya dace inda ya ke cewar hukumarsa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an yi sahihin zabe a kasar.

Dangane da karbar katuna na zabe na dindindin kuwa, shugaban hukumar zaben ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin kowa ya samu nasa kafin ranar zabe kuma ya ce suna nan kam bakansu wajen ganin an yi amfani da na'urar nan ta Card Reader a zaben wanda jam'iyyar PDP da ke mulkin kasar ke son ganin ba a yi amfani da shi ba.

DW.COM