Attahiru Jega tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta, wanda ya jagoranci shirya zabukan shekara ta 2011 da kuma 2015.
Sunan Jega ya kara fitowa, inda ya zama shugaban hukumar zabe na farko da ya shirya zaben da jam'iyyar adawa ta kwace madafun iko daga jam'iyya mai mulki a shekara ta 2015. Kafin zama shugaban hukumar zabe a matsayin farfesa ya jagoranci jami'ar Bayero da ke Kano, ya kuma taba zama shugaban kungiyar malaman jami'o'i ta kasa.