1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sace dalibai ya dauki hankulan jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
November 9, 2018

Jaridun Jamus sun yi nazarin batutuwa da suka auku a kasashen Afirka amma batun sace dalibai akalla 79 da wasu 'yan bindiga suka yi a kasar Kamaru a farkon wannna makon mai karewa ya ja hankulan akasarin jaridun kasar.

https://p.dw.com/p/37xeV
Symbolbild Deutschland Medien
Hoto: imago/Ralph Peters

Jaridar Neue Zürcher Zeitung wanda ta rubuta sharhi akan daliban na 79 da aka sace a Kamaru mai taken "Masu garkuwa da yara sun bukaci a rufe makaranta" Jaridar ta cigaba da cewar a ranar Litinin da ta gabata ne wasu mutane suka sace daliban wata makarantar sakandare da ke garin Bamenda guda 79 da malamansu guda uku. Bamenda na zama babban birnin yankin Arewa maso Yammaci, wanda gaminsa da Kudu maso Yammacin Kamarun ne ke zama yankunan 'yan aware na masu magana da harshen Turancin Ingilishi, wadanda kuma ke fadan fafutukar ballewa domin samun 'yancin cin gashin kai.

Kamerun Nigeria Angst vor Boko Haram in Fotokol
Hoto: KAZE/AFP/Getty Images

Yaran da aka sace na 'yan kwanaki kafin a sako su dai, babu abun da masu sacensu suka nema face bukatar a rufe makarantar. Sace daliban na Bamenda ya auku ne a jajiberen ranar rantsar da shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya da ya samu zarcewa kan mukaminsa na mulki a karo na bakwai. A ranar 7 ga watan Oktoba ne dai aka zabi shugaban mai shekaru 85 da haihuwa a karo na bakwai, domin yin wani wa'adin na shekaru bakwai akan wannan kujera da ya kasance na tsawon shekaru 36.

Dan takarar adawa Maurice Kamto ya yi fatali da sakamakon zaben, inda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa, bayan shugaba Biya ya sha rantsuwar cigaba da mulkin Kamaru. Matakin shugaban Kamarun na yin takara karo na bakwai ya harzuka 'yan awaren kasar, tare da ruruta rikici a yankin, daura da kauracewa zaben da 'yan awaren suka yi.

Sharhi kan zaben Madagaska

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung tsokaci ta yi game da zaben shugaban kasar Madagaska da aka gudanar a ranarl Larabar wannan makon. A labarinta mai taken " Wajibi ne Hery Rajaonarimampianina ya yi fargaba dangane da yunkurinsa na neman zarcewa kan kujerar mulki." jaridar ta ce fitattu daga cikin 'yan takarar sun kasance tsoffin shugabanninta, wadanda adawarsu a baya ta jefa wannan tsibiri cikin wani wadi na tsaka mai wuya.

Abun takaici shi ne tsibirin na fama da rudani na rashin shugabanci, wanda ya jefa tattalin arzikinta cikin halin kaka nika yi. A lokacin da ta samu 'yancin kai a shekarun 1960, Madagaska ta kasance kamar Malasiya da brazil, sai dai a yau ta kasance daya daga cikin matalauta. Kashi 90 daga cikin al'ummar miliyan 25 ke rayuka cikin matsanancin talauci.

Uganda - Bobi Wine (Sänger) mit Krücken in Gerichtssaal in Gulu
Hoto: Getty Images/AFP

Da wuya hakar Bobi Wine ta cimma ruwa

Jaridar Berliner Zeitung kuwa sharhi ta rubuta game da yunkurin fitaccen mawakin rege Bobi Wine na takarar shugabancin kasar Yuganda.A sharhin nata mai taken "babban makiyi" jaridar ta ce zai zame abu mawuyaci mawakin da ya rikide zuwa dan siyasa mai shekaru 36 da haihuwa ya cimma wannan buri da ya sanya a gaba.

A watan agusta nedai sojojin kasar da ke yankin gabashin Afirka suka yi wa Robert Kyagulanyi Ssentamu da aka fi sani da Bobi Wine dirar mikiya, inda suka kusan hallaka shi. Komawarsa Yuganda bayan jinyar makonni uku a wani asibitin kasar Amurka ke da wuya, jami'an tsaro suka cafkeshi. Shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 74 da haihuwa mai tsarin mulki irin na sai madi ka ture na yi wa Bobi Wine kallon babbar makiyi.