1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kuncin rayuwa a kudancin Kamaru, karancin abinci a Sudan

Zainab Mohammed Abubakar MNA
October 8, 2021

Halin da ake ciki na rashin kula da lafiyar al'umma a kudancin Kamaru da karancin abinci a Sudan da bukin tantance fina-finai a Somaliya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/41SXi
Kamerun Garoua Boulai | Flüchtlinge aus der Zentralafrikanischen Republik
Hoto: Joel Kouam/REUTERS

Zamu yaye kallabin shirin na wannan mako ne da labarin da jaridar Die Zeit ta wallafa mai taken "Wadanda aka mance da su". A kudancin Kamaru yankin da ba a iya zuwa, al'umma na rayuwa ba tare da kulawa da lafiyarsu ba.

Godiya ga Rene Staheli dan asalin kasar Switzerland da ya kawo wa mazauna wannan sansani na gandun daji tallafi wajen yaki da wasu cututtuka da babu wanda ya san da su a sauran sassan duniya. Tare da tawagarsa ta likitoci da jami'an kiwon lafiya Rene Staheli mai shekaru 65, sun bazama cikin kungurmin dajin da ke yankin gabashin Kamaru.

Ya ce: "Ko wadannan mutane na da lafiya ko babu, wajibi ne a kula da su. Kuma kamata ya yi a ce barkewar annobar corona ta kasance darasi ga lamuran lafiya a duniya baki daya." Rene Staheli dai na jagorantar wata kungiya mai zaman kanta a kasar Switzerland, wadda ke yaki da cututtuka da ke da nasaba da talauci.

Ya je yankin kudancin Kamarun ne biyo bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya baiwa dukkan dan Adam 'yancin a kula da lafiyarsa. Ta karkashin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Majalisar Dinkin Duniya na muradin kawo karshen annobar cututtuka da mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.

Südsudan Kandak 2018 | Frau & Sorghumhirsen nach Essensabwurf WFP
Hoto: Sam Mednick/AP Photo/picture-alliance

"Karancin abinci na kara kamari a Sudan biyo bayan toshe tashar jirgin ruwa mafi girma a kasar." Da haka ne jaridar Neues Deutschland ta bude sharhin da ta rubuta game da halin da wannan kasa ta tsinci kanta ciki na rashin kwanciyar hankali shekara guda da rabi bayan hambarar da gwamnati mai salon na sai-madi-ka-ture ta Omar Hassan al-Bashir.

Sudan din dai na fama da rigingimun neman madafun iko tsakanin kungiyoyin kabilu da 'yan tawaye daura da majalisar mulkin rikon kwarya. Tsawon makonni 'yan Beja, kabilar da al'ummarta ta fi yawa a yankin gabashin Sudan din da ke gabar tekun Bahar Maliya, suka toshe babbar tashar jiragen ruwa mafi girma a wata zanga-zangar da suka kira ta neman ingantuwar tattalin arziki.

Yanzu haka dai gwamnatin Sudan din ta yi gargadin cewar, kasar na fuskantar barazanar karewar magunguna da alkama da man fetur, saboda toshe tashar jiragen ruwan. A wata sanarwar da majalisar mulkin Sudan din ta wallafa a ranar Lahadi, ta ce 'yan kabilar Beja na da 'yancin gudanar da zanga-zanga, amma fa cikin lumana. A lokaci guda kuma ta yi gargadin cewa, toshe manyan hanyoyin da ke hada yankunan kasar ya haifar da illa ga al'ummar Sudan din.

Somalia Mogadischu | National Theatre | Erste Aufführung
Hoto: Abdirahman Yusuf/AFP/Getty Images

Daga batun barazanar karancin abinci a Sudan bari mu juya duniyar shakatawa. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta dauke mu ne zuwa yankin kahon Afirka, inda ta wallafa labari kan bukin tantance fina-finai a karon farko cikin shekaru 30 a kasar Somaliya.

Jaridar ta ce, sake gyaran dandalin nuna fina-finai na kasa da ke tsakiyar birnin Mogadisho, kyakkyawan fata ne ga sake farfadowar harkokin al'adu da nishadi a wannan kasa da yaki ya daidaita. Tsawon shekaru 30 ke nan ba a taba nuna wani fim ba, sai a ranar Larabar da ta gabata da babban dakin taron ya sake cika makil da 'yan kallo a karon farko tun shekara ta 1991.

Dandazon jami'an tsaro a kewayen katafaren ginin, na tunatarwa da jama'a cewar har yanzu wasu yankunan Somaliya na fama da yakin basasa. Batu kuma da ya jefa 'yan kallo 1,500 da ke dakin taron cikin rudani. Sai dai duk da haka daga lokaci zuwa lokaci sukan zaro wayoyinsu don daukar hoton fina-finan da ake nunawa, a matsayin farin ciki na wannan sabon babi a rayuwarsu.