1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan ta dauki matakin karawa sojinta karfi

Zulaiha Abubakar
December 18, 2018

Gwamnatin Japan ta sanar da amincewar mayar da wasu manyan jiragen ruwa zuwa jiragen dakon jiragen yaki cikin tsare-tsaren shekaru biyar don karawa Sojojin kasar da Firaministan kasar ya kaddamar.

https://p.dw.com/p/3AHmk
Shinzo Abe
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Images/E. Hoshiko

Sanarwar ta kara da cewar daukar wannan mataki ya zama dole sakamakon kalubalen tsaron da kasar ta Japan ke fuskanta wadanda suka hada da tsamin dangantaka da Koriya ta Arewa da kuma yadda Sojojin Chaina suke ketara yankunan Japan a cikin sirri.

Tun da fari Firaminista Shinzo Abe ya baiyana cewar shirye-shirye sun kammala don sayo wasu jiragen yaki samfirin F35B da yawansu ya kai 42 don aiyukan tsaro,duk kuwa da cewar cinikin makaman na zuwa ne bayan ingantuwar alaka tsakanin kasar da Amirka.