Janye matsugunan yahudawa a gabar yamma | Labarai | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janye matsugunan yahudawa a gabar yamma

Mukaddashin P/M Israila Ehud Olmert ya yi alkawarin Idan ya ci zabe, zai janye matsugunan yahudawa daga wasu yankuna na Palasdinawa da Israila ta mamaye a gabar yamma da kogin Jordan. An ruwaito mai baiwa mukaddashin P/M shawara kan shaánin tsaro Avi Dichter na cewa shirin ya tanadi maido da yahudawan dake zaune a wasu kebabbun wurare ya zuwa manyan birane. Ehud Olmert ya baiyana shata iyakokin kasar Bani yahud da cewa shi ne babban abin da zai maida hankali a kai idan ya yi nasarar lashe zabe. Kuriár jin raáyin jamaá na nuni da cewa jamíyar sa ta Kadima na da alamun samun rinjaye a zaben wanda zaá gudanar a ranar 28 ga wannan watan.