Janar Petraeus ya ba da bahasi a gaban majalisar dokokin Amirka | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janar Petraeus ya ba da bahasi a gaban majalisar dokokin Amirka

Babban kwamandan Amirka a Iraqi Janar David Petraeus ya fadawa majalisar dokokin Amirka cewa an cimma da yawa daga cikin manufofin kara yawan dakarun kasar a Iraqi. Petraeus ya bayyana haka ne lokacin da yake ba da bahasi akan manufofin shugaba GWB dangane da kara yawan sojojin kasar a Iraqi. Ya ce yayi imani ana iya rage yawan sojoji izuwa yawansu gabanin a kara su wato dubu 160 kafin lokacin bazara na badi. A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa a kan rahoton ci-gaba a Iraqi da jakadan Amirka a Iraqi Ryan Crocker, shugaban kwamitin dake kula da harkokin ketare na majalisar dokokin Amirka Tom Lantos cewa yayi.

O-Ton Lantos:

Ya ce “Halin da ake ciki a Iraqi na neman a canza alkibla cikin gaggawa. Dole ne mu janye daga Iraqi don mu shafawa kanmu da ma Iradi lafiya. Lokaci yayi da ya kamata mu janye.”