1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shehu Shagari ya rasu

December 29, 2018

Tsohon shugaban Najeriya a jamhuriyar ta biyu Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari ya rasu ya na da shekaru 93 a duniya, sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya a babban asibitin kasar da ke Abuja.

https://p.dw.com/p/3AlNl
Nigeria Abuja Nationalrat
Tshohon shugaban Najeriya marigayi Shehu Shagari daga hagu sanye da fararen kaya, tare da wasu tsoffin shugabannin kasarHoto: DW/U. Musa

Dimbin mutane daga ciki da wajen kasar ne suka halarci sallar janai’zar tsohon shugaban Najeriyar Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari da aka gudanar da misalin karfe biyu agogon kasar, a mahaifarsa da ke garin Shagari. Tsohon shugaban kasar dai tarihi ba zai iya mantashi ba, musamman a fannin Dimukuradiyya. An haifi Shehu Shagari ne a ranar 25 ga watan Fabarairun shekara ta 1925 a karamar hukumar Shagari da ke jihar Sakkwato. Bayan kammala karatunsa, marigayin ya soma aikin koyarwa kafin daga bisani ya shiga harkokin siyasa, lamarin da ya kai shi ga zama shugaban kasar Najeriya a jamhuriya ta biyu, bayan da ya lashe zabe a shekarar 1979.

Marigayin ya rasa shugabancin Najeriyar, biyo bayan wani juyin mulkin soji a shekarun 1983, wanda shugaban kasar mai ci yanzu Muhammadu Buhari ya yi masa, a lokacin yana cikin kaki. Wasu dai na yi wa Alhaji Shehu Shagari kallon mutumin da ke da matukar tasiri ga dimukuraddiyar Najeriya. Marigayi Shehu Shagari ya rasu ne a ranar Jumma'a 28 ga wannan wata na Disamba da muke ciki da misalin karfe shida da rabi na yamma a babban asibitin kasa da ke Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya mai nasaba da cutar limoniya. Ya rasu yana da shekaru 93 a duniya kuma ya bar matan aure guda biyu da 'ya'ya 19, mata 11 maza takwas, kuma an binne shi ne a gidan sa da ke garin na Shagari  cikin jihar Sokoto.