1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi a dakatar da fadan Siriya

Ramatu Garba Baba
October 19, 2019

Kurdawa mazauna birnin Cologne sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin da gwamnatin Turkiyya ta dauka na afkawa mayakan Kurdawa da ke yankin arewa maso gabashin Siriya.

https://p.dw.com/p/3RZAr
Köln | Proteste der Kurden gegen der türkischen Militäroffensive in Syrien
Hoto: Reuters/T. Schmuelgen

Mutane kimanin dubu biyar ne suka shiga zanga-zangar a wannan Asabar, bayan da suka soki matakin afkawa 'yan tawayen Kurdawa a arewa maso gabashin Siriya. Sun dai ja hankalin gwamnatin Ankara kan dakatar da fadan da tuni ya haifar da matsaloli ga fararen hula tare da bai wa mayakan IS kafar tserewa daga gidajen yari.

'Yan sanda sun dauki matakin kasancewa cikin shiri don kwantar da duk wata tarzoma, sai dai kawo yanzu masu zanga-zangar sun ci gaba da baiyana manufofinsu cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba. Jamus ta kasance gida ga dubban Turkawa da Kurdawa da basa ga maciji da juna amma suka ci gaba da zaman lafiya a kasar ta Jamus ciki.

Bayan matsin lamba ga shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan kan ya dakatar da farmakin da dakarunsa ke kai wa a yankin Kurdawa ya dai amince da tsagaita wuta.