Jamus za ta karbi ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 09.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Jamus ta nuna aniyar karbar mata da yara

Jamus za ta karbi 'yan gudun hijira

Kungiyar Tarayyar Turai za ta gana da Shugaba Erdoghan domin warware takaddamar da ta kunno kai kan 'yan gudun hijirar da ke son shiga nahiyar Turai ta kasar Girka.

A wannan Litinin za a yi wani zama a tsakanin Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da wasu shugabanin kungiyar tarayyar Turai ta EU kan 'yan gudun hijirar da aka hana shiga Turai ta kasar Girka. Taron na birnin Brussels zai nemi samar da mafita da kawo karshen arangama a tsakanin 'yan gudun hijira da ke yunkurin shiga Girka da jami'an tsaron kasar.

Sabon rikici kan 'yan gudun hijira ya kunno kai a tsakanin EU da Turkiyya a makon da ya gabata, bayan da Turkiyyyan ta bude musu hanyar da a baya EU ta bukaci a toshe.

Tuni Jamus ta yi tayin karbar 'yan gudun hijira akalla 1,500 akasarinsu mata da yara daga cikin wadanda aka tsugunar a sansanin 'yan gudun hijirar da ke Girka.