1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: Bundesliga ta dawo

May 6, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a jawabinta na wannan Laraba ta ce sun amince a dawo da wasannin Bundesliga a cikin wannan watan a saboda lafawa da cutar coronavirus ta yi a kasar.

https://p.dw.com/p/3bs0x
Deutschland Berlin Pressekonferenz Coronavirus | Angela Merkel
Hoto: Reuters/M. Sohn

Merkel ta ce yanzu ya rage ga hukumar tsara wasannin kasar ta bayyana ranar da za ta bude Bundesliga. Kazalika shugabar ta ce daga yanzu an amince duk wani shago komi kankantarsa ya bude; ya ci gaba da sana'arsa. An kuma amince yanzu 'yan uwa da abokan arziki za su iya kai wa juna ziyara.

Wadannan matakai dai sun biyo bayan nasara da Jamus ke yi a kan annobar coronavirus, inda Merkel din ta ce:

''Yanzu kasar Jamus ta kai lokacin da za ta iya bugar kirjin cewa ta cimma kudurinta na rage yaduwar coronavirus, mun kuma yi wa tsarin kiwon lafiyar kasarmu gagarumin garambawal.''

Sai dai duk da haka ta ce mutanen Jamus za su ci gaba da nesa-nesa da juna har ranar 5 ga watan Yuni, domin takaita yaduwar cutar, amma ba wai don cutar tana musu barazana ba.