Jamus: Shekara guda da harin kasuwar Kirismeti | Labarai | DW | 27.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Shekara guda da harin kasuwar Kirismeti

Daruruwan mutane daga sassan Jamus sun kai ziyara kasuwar Kirismeti a birnin Berlin inda aka kai harin ta'addancin da ya hallaka rayukan mutane 12 da raunata wasu fiye da 70.

Ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya shawarci jama'a kan yin taka tsantsan sai dai ya ce su gudanar da harkokinsu cikin walwala. An dauki kwararan matakan tsaro don kare rayuwar al'umma. 

A watan Disambar bara ne dai aka kai wannan harin wanda Kungiyar IS ta dauki alhakinsa.

Anis Amri dan kasar Tunisiya ya kutsa da wata katuwar mota cikin jama'ar da ke tsakiyar hada hada a kasuwar gabanin bikin kirsimeti. An gudanar da addu'oi a wannan Litinin a cocin nan mai dadadden tarihi na Kaiser-Wilhelm da ke kusa da kasuwar