1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Faransa na fatan a rage ɗumamar yanayi

Abdourahamane HassaneMay 19, 2015

Angela Merkel da Francois Hollande sun yi kiran da a cimma yarjejeniyar rage iskan hayaƙin da kamfanoni ke fitarwa a duniya.

https://p.dw.com/p/1FShO
Deutschland 6. Petersberger Klimadialog in Berlin
Hoto: T. Schwarz/AFP/Getty Images

Shugabanin ƙasashen Faransa da Jamus wato Francois Hollande da Angela Merkel da ke halartar wani taro kan canjin yanayi a Berlin,sun yi kiran da a cimma wata yarjejeniya wacce ka iya taimaka wa a rage ɗumamar yanyin da ake samu a duniya.

A sakamakon hayaƙin iskan guba da kamfanoni da masana'antu suka kan fitarwa galibi a ciki ƙasashe masu arziki.Taron wanda ke samun halartar wakilai daga ƙasashen duniya kusan 35 na ƙoƙarin samun daidaituwar baƙi a kan batun,gabannin taron Majalisar Ɗinkin Ɗuniya a kan ɗumamayar yanayi da za a yi a birnin Paris nan gaba a cikin watan Disamba da ke tafe.