Jam′iyyar AKP ta lashe zabe a Turkiya | Siyasa | DW | 02.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'iyyar AKP ta lashe zabe a Turkiya

Jam'iyyun adawa a Turkiya na nuna takaicinsu dangane da nasarar da jam'iyyar AKP mai mulki ta samu a zaben kasar da ya gudana a karshen mako.

Al'ummar Turkiya na murnar sakamakon zabe.

Al'ummar Turkiya na murnar sakamakon zabe.

Ko da yake sakamakon zaben ya zo wa mutane da yawa a ba-zata, amma idan aka dubi abin da idanun basira, to ba abin mamaki ba ne. Ugur Demirkan na kungiyar matasan jam'iyyar CHP bai ji dadin sakamakon zaben ba. Jam'iyyarsa ta shafe tsawon lokaci tana lashe kuri'u a mazabar Besiktas, inda sau da yawa ta kan samu kashi 60 cikin 100 na kuri'u a wannan mazaba, abin da ya basu kwarin gwiwar cewa a wannan karo ma za su taka rawar gani. Ga abin da Demirkan ke cewa:

Haka ta gaza cimma ruwa

Ya ce: "Jam'iyyata ta tabka kurakurai a zabukan da suka gabata. Amma a wannan karo mun yi komai dai-dai, mun gabatar da shirye-shiryen zabe masu kayatarwa."

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.

Sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, domin jam'iyyar ta CHP ta yi asarar kashi uku cikin 100 na yawan kuri'unta, inda a kasar baki daya ta tashi da kashi 25 cikin 100. Jam'iyyar da ta lashe zaben kai tsaye ita ce AKP ta Firaminista Ahmet Davutoglu, inda sakamakon wucin gadi ya nuna tana da kaso 50 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, abin da a cewar Kristian Brakel na gidauniyar Heinrich-Böll da ke birnin Istanbul, AKP din ta karbe wasu kuri'u daga CHP da kuma jam'iyyar HDP ta Kurdawa masu kishin kasa.

Hasashen rashin nasara ga AKP

Gabanin zaben kusan dukkan cibiyoyin nazarin zabe sun yi hasashen cewa sakamakon zaben ba zai yi wa AKP kyau ba. Amma matakan da jam'iyyar ta dauka musamman na nuna ba sani ba sabo kan kungiyar PKK da batun kishin kasa da farfado da tattalin arziki sun ja hankalin masu zabe.

Türkei Selahattin Demirtas Shugaban jam'iyyar HDP mai adawa a Turkiya.

Türkei Selahattin Demirtas Shugaban jam'iyyar HDP mai adawa a Turkiya.

A shelkwatar jam'iyyar HDP ta Kurdawa da ke unguwar talakawa a birnin Isltanbul kusan ana cikin zaman makoki ne. Jam'iyyar wadda ta samu kaso10 cikin 100 ta yi asarar kashi uku cikin 100 idan aka kwatanta da yawan kuri'un da ta samu a zaben watan Yunin da ya gabata. Hecar Akdemir ya nuna takaicinsa yana mai cewa:

"Duk abubuwan na da alaka da jam'iyyar AKP musamman ma Erdogan. Ba mu yarda da shi ba. Mun san shi mun kuma san abin da yake yi. Na yanke kauna da zabe. Tsarin gaba dayansa ba ya aiki."

Sai dai Samuel Vesterbye na wata kungiya mai zaman kanta da ake kira "Young Friends of Turkey" ya kalubalanci wannan furuci na Akdemir.

Ya ce: "Bai kamata mu ga wannan tamkar jam'iyyun siyasa a Turkiya sun bace ne ba. An gudanar da zabe, wasu sun yi asarar kuri'u wasu kuma sun samu. Saboda haka bisa tsarin demokradiyya ba zan iya cewa demokradiyya ta yi rauni a Turkiyya ba."

Jm'iyyar HDP dai za ta samu wakilci a majalisar dokoki kamar yadda ya kasance watanni biyar baya, amma AKP ce za ta kasance wuka da nama a fagen siyasar kasar ta Turkiyya. Wannan kuwa zai ba ta cikakken ikon daukar karin nauyi, musamman game da rikicin Kurdawa da manazarta harkokin siyasa suka ce ya kasance wani zakaran gwajin dafin manufar jam'iyyar ta AKP.

Sauti da bidiyo akan labarin