Jam′iyya mai mulkin Turkiya ta samu rinjaye a zaben | Labarai | DW | 02.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyya mai mulkin Turkiya ta samu rinjaye a zaben

Firaminista Ahmet Davutoglu ya samu babbar nasara bayan da jam'iyyarsa ta AKP ta samu kashi 49 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben 'yan majalisa.

Parteitag AKP Türkei Ahmet Davutoglu Plakat Flagge Ankara

Ahmet Davutoglu

Jam'iyya mai mulki a kasar Turkiya ta samu gagarumin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi a jiya Lahadi abin da zai ba ta damar kafa gwamnati bayan da a watanni biyar da suka gabata ta rasa rinjaye.

A cewar rahoton da gidan talabijin TRT a kasar ta Turkiya ya fitar, Firaminista Ahmet Davutoglu ya samu babbar nasara bayan da jam'iyyarsa ta AKP ta samu kashi 49 cikin dari na kuri'un da aka kada, abin da ke nuna cewa za ta samu kujerun majalisa 316 daga cikin 550.

Bayan kammala kidaya kashi 99 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben 'yan majalisar kasar, hakan dai na nuna cewa jam'iyyar ta AKP ta samu rinjaye a kujerun majalisar 550.

Tuni dai Firaminista Davutuglu ya bukaci sauran al'ummar kasar su rungumi junansu:

"Ina kira ga daukacin al'ummar kasar Turkiya ba tare da banbancin jam'iyya ba su hada kansu, sannan wadanda za su shiga majalisa su samar da sabon kundin tsarin mulkin kasa da zai haifar da gwamnati da tsarin siyasa mai inganci bayan sauya kundin tsarin mulkin kasar da aka gada tun bayan mulkin soji."