Jami′an tsaron Italiya sun bindige Anis Amri a Milan | BATUTUWA | DW | 23.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Jami'an tsaron Italiya sun bindige Anis Amri a Milan

'Yan sanda a birnin Milan na kasar Italiya, sun sanar da harbe har lahira mutumin nan da ake nema ruwa a jallo bisa zarginsa da ake da hannu a harin kasuwar Kirsimeti ta birnin Berlin na nan Jamus.

Italien Mutmaßlicher Berliner Attentäter in Mailand getötet (picture-alliance/dpa/Daniele Bennati/B&V)

Jami'an tsaro masu bincike a Birnin Milan na Italiya

Hukumomi a kasar Italiya suka ce a wannan Juma'ar ce aka harbe Anis Amri lokacin da 'yan sanda da ke yin sintiri suka tinkari inda ya ke a birnin Milan don tambayarsa takardun shaidar izinin zama a kasar. Isa wurinsa ke da wuya kamar yadda suka shaida wa manema labarai sai Amri din ya zaro bindiga daga jakarsa ya bude wa wani dan sanda wuta inda ya jikkata shi, lamarin da ya sanya sauran 'yan sanda da ke tare da shi suka maida martani nan take kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Ministan harkokin cikin gidan Italiya Marco Minniti ya ce ko shakka babu jami'ansu sun hallaka Amri wanda kasashen Turai ke nema ruwa a jallo bisa harin na Berlin inda yake cewa:

 

Italien Terrorverdächtiger Anis Amri in Mailand erschossen (picture-alliance/AP Photo/G. Borgia)

Ministan cikin gida na Italiya Marco Minniti

"Ba tare da wata tantama ba, mutumin da jami'an mu suka hallaka Anis Amri ne wanda ake zargi da kai harin ta'addanci a birnin Berlin. Wannan nasara da aka samu ta biyo bayan zuzzurfan bincike da jami'anmu suka gabatar."

 

Fitar wannan labari na kisan Amri da misalin karfe uku na daren jiya ya sanya hukumomi a nan Jamus da ke nemansa ruwa a jallo bayyana jin dadinsu dangane da wannan nasara da aka cimma. Tobias Plate da ya yi magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Jamus kan wannan batu, ya ce yanzu hankulansu za su kwanta tunda wanda ake nema ido rufe kan wannan hari da ya hallaka mutane ya rasu. A daura da wadan nan kalamai na Mr. Plate, Firaministan Italiya Paolo Gentiloni ya ce tuni ma ya kira shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, inda ya shaida mata cewar jami'ansu sun hallaka Amri, kana ya yi mata karin haske kan yadda lamarin ya wakana.

" Na shaida wa Merkel da safiyar yau cewar an kashe Anis Amri a kusa da Milan. Wannan abu da ya faru ya kara nuna muhimmancin da ke akwai na cigaba da sanya idanu a kasashenmu da ma hadin kai da ya kamata a ce an kara samu tsakanin jami'an tsaronmu."

Italien Terrorverdächtiger Anis Amri in Mailand erschossen Premierminister Paolo Gentiloni (picture alliance / Giuseppe Lami/ANSA/dpa)

Firaministan kasar Italiya Paolo Gentiloni

Gentolini din na wadannan kalamai ne yayin da ya kira wani taron manema labarai don yin karin haske game da kisan na Anis Amri, inda ya ce duk da cewar an kashe mutumin, ba za su saki jiki ba domin kuwa barazana ta ta'addanci ba aba ce da za a dauka da wasa ba. Yayin da wannan labari ke fita, hada-hada a kasuwar Kirsimiti ta Berlin wadda aka kai wa hari na ci gaba da wakana, inda jama'a ke gudanar da harkokinsu na saye da sayarwa gabannin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara da ke tafe, yayin da jami'an tsaro a sauran sassan Jamus ke ci gaba da yin bincike da nufin bankado wanda ke da hannu a wannan hari, da ma sauran hare-hare da ake zaton wasu bata-gari na shirin kai wa musamman a ranar Kirsimeti.

 

Sauti da bidiyo akan labarin