Jamian tsaron Iraqi sun harbe mutane hudu a zanga zanga | Labarai | DW | 01.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamian tsaron Iraqi sun harbe mutane hudu a zanga zanga

Irq/protest

Jamian tsaro a Iraqi sun harbe mutanme hudu a yayin wata zanga zangar adawa da karin farashin man fetur,bayanda masu zanga zangar suka fara kona motoci da gidajen sayarda mai, a kusa da birnin Kirkuk da ake hako mai.

Iraqin dai wadda itace ta uku a duniya a arzikin mai alummarta suna fuskantar karancinsa da kuma karin farashin da hukumomi sukayi a karkashin wata yarjejeniya da suka yi da Asusun bada lamuni na duniya.

Sakamakon matsalar man da kuma kara farshin da dama daga cikin jamaar kasar da sukayi zaben yan majalisar kasar a watan daya gabata suna korafi da cewa an yaudare su.

A yanzu dai an kafa dokar hana yawan dare a yankin da aka kashe mutanen.