1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Zargin tallafi ga 'yan ta'adda

Zulaiha Abubakar
October 2, 2018

Jam'an 'yan sanda a kasar Turkiyya sun tsare sama da mutane 200 a ci gaba da kamen mutanen da ke da hannu cikin aikewa da  'yan asalin kasar Iran mazauna Amirka kudade ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/35sCk
Türkei Präsident Erdogan
Hoto: Getty Images/AFP/A. Weiss

Tun bayan da babbar kotun birnin Istanbul ta bayar da umarnin kamo mutanen da adadin su ya kai 417, jami'an tsaro suka yi nasarar cafke 216 cikin birane 40 da ke fadin kasar. Ana tuhumar wadanda aka samu da hannu cikin aika kudaden da taimakon kungiyoyin ta'adda.

Sakamakon wani bincike da kasar ta Turkiyya ta gudanar tun a shekara ta 2017, ya bankado kudi kimanin Dalar Amirka miliyan 400, wadanda aka tura bankunan da yawansu yakai dubu 28 a kasashen ketare duk kuwa da cewar kasar ba ta bayyana sunayen mutanen da aka turawa kudaden ba. A farkon wanann shekara ne dai gwamnatin kasar Amirka ta gurfanar da Mehmet Hakan Atilla mataimakin shugaban bankin Halkbank na kasar Turkiyya a gaban kuliya, sakamakon zargin sa da taimakon kasar Iran ketara takunkumin da Amirka ta kakaba mata.