1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin rage zaman dardar tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Mohammad Nasiru Awal ZMA
February 25, 2023

Kasar Jordan ta gaiyaci wakilan Isra'ila da Falasdinu a wata tattaunawa da ke da burin rage zaman dardar tsakaninn bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/4NzAW
Yammacin Kogin Jordan | Samamen sojojin Isra'ila a NablusHoto: Zain Jaafar/AFP/Getty Images

Bayan tarzomar baya-bayan nan a yankunan Falasdinawa, wakilan Isra'ila da na Falasdinawa za su yi wata tattaunawa a kasar Jordan a ranar Lahadi. Manufar tattaunawar da aka ce ta tsaro da siyasa ce, ita ce samar da yarda tsakanin bangarorin biyu, inji wani wakilin gwamnatin Jordan a wannan Asabar.

Jami'in ya kara da cewa an gaiyaci wakilan kasashen Amirka da Masar a taron da zai gudana a birnin Akaba, taron kuma da zai taimaka a rage zaman dardar tsakaninn Isra'ila da Falasdinu. Tattunawar dai na daga cikin yunkurin da Jordan ke yi na ganin Isra'ila ta daina daukar matakai na gaban kai tare kuma da rage yawan tashe-tashen hankula a yankin.

Alkalumman Falasdinu sun ce akalla mutane 11 ciki harv da wani dan shekara 16  aka kashe sannu wasu kimanin 80 sun jikkata a wani samame da sojojin Isra'ila suka kai a birnin Nablus a ranar Laraba da ta gabata. Samamen shi ne irinsa mafi muni da Isra'ila ta yi a Yammacin Kogin Jordan tun shekarar 2005. A ranar Alhamis da ta gabata a harba rokoki da dama daga Zirin Gaza zuwa cikin Isra'ila.