Jami´a tsaron Faransa sun kasa kawo karshen tarzomar matasa a kasar | Labarai | DW | 06.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jami´a tsaron Faransa sun kasa kawo karshen tarzomar matasa a kasar

´Yan sandan Faransa sun kasa shawo kan tashe tashen hankula da suka addabi birnin Paris da kewaye. A dare na 10 a jere an yi ta kone kone da tarzoma a unguwannin dake wajen babban birnin na Faransa da kuma a wasu birane na kasar. Kamar dai a sauran tashe tashen hankulan a daren jiya ma daruruwan matasa masu tarzoma sun yi ta cunnawa motoci da gine gine gwamnati da kuma kantuna wuta. Ministan harkokin cikin gidan Faransa Nicolas Sarkozy ya ba da sanarwar cewa jami´an tsaro zasu dauki matakan ba sani ba sabo akan masu ta da zaune tsayen. Bayan wani taron gaggawa a karakshin jagorancin FM Dominique de Villepin, Sarkozy ya nunar da cewa gwamnati ta lashi takobin murkushe wannan rikici. Shugabannin siyasa a kasar sun yi kira ga shugaba Jaques Chirac da ya yiwa jama´ar kasar jawabi don yin kira da a kwantar da hankali. Yanzu haka dai wasu mazauna unguwannin da ake fama da rigingimun sun fara nuna kosawar su da rikice-rikicen.