Jagoran adawa a Rasha ya kira gangami | Labarai | DW | 28.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran adawa a Rasha ya kira gangami

Jagoran adawa a kasar Rasha Alexei Navalny da magoya bayansa sun sha alwashin fita gangami a wannan rana ta Lahadi don nuna adawa da shirin zabe a fadin kasar. Zaben da suka bayyana da cewa mara fuska.

Russland Oppositioneller Nawalny kandidiert als Präsidentenbewerber (Reuters/M. Shemetov)

Alexei Navalny da matarsa a gaba

Dan siyasar mai shekaru 41 Alexei Navalny ya yi kira ga al'ummar kasar ta Rasha su fito gangamin adawa da mahukuntan da ke shirin zabe kuma su kauracewa zaben da za a yi ranar 18 ga watan Maris duk kuwa da fargabar da ake da ita cewa daga bangaren mahukunta sun shirya kame-kamen 'yan adawar.

A cewar Navalny an tsara gudanar da gangamin a birane sama da 100 ciki har da birnin Moscow da Saint Petersburg inda ake sa ran za a yi taho mu gama tsakanin 'yan adawar masu zanga-zanga da jami'an 'yan sanda.

Jagoran adawar dai Navalny ya bayyana a fefen bidiyo yana cewa sun gaji da shekaru 18 na mulkin danniya da sace-sacen dukiya na masu mulki a kasar ta Rasha a yanzu.