Italiya zata bawa Abdul Rahman mafaka na siyasa | Labarai | DW | 30.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya zata bawa Abdul Rahman mafaka na siyasa

A yau ne ake saran cewa dan kasar Afganistan dake fuskantar hukuncin kisa sakamakon Ridda da yayi zuwa addinin christa,zai nemi mafakar siyasa a hukumance a kasar italiya.A yanzu haka dai Abdul Rahman ya wata mubuya na sirri a kasar bayan saceshi daga afganistan din a asirce.Rahotannin maaikar harkokin cikin gida na Italiyan na nuni dacewa tun da sanyin safiyar jiya laraba ne ya isa birnin Rome,daga baya ne Premier Silvio Berlusconi ya sanar dacewa ,a shirye suke su bashi mafaka ,saboda irin bajinta da ya nuna.A yau ne ake saran abdul Rahman zai bukaci mafakar a hukumance,kuma tuni majalisar zartarwar Italiyan ta amince da hakan.Batun hukuncin da ake yanke wa Abdul Rahman dai ya dauki hankalin duniya a yan kwanakin nan,inda kasashen yammaci da Amurka suka bayyana adawansu dashi.

 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7A
 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu7A