1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta ce ISWAP ta sako jami'an hukumar

Abdourahamane Hassane
June 16, 2021

Wata majiya ta MDD ta ce kungiyar ISWAP ta saki mutane guda goma da take  yin garkuwa da su a ciki har da ma'aikatan kungiyoyin ayyukan jin kai guda bakwai a arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3v3pg
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

An dai kai ga nasarar sakin mutanen ne bayan kwashe tsawon makwannin ana tattaunawa da masu yin garkuwar. Daga cikin wadanda aka sako har' da wani jami'in hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya PAM da na kungiyar agaji ta Red Cross da kuma wani ma'aikacin hukumar 'yan gudun hjirA ta MDD wadanda aka sace tun cikin watan Disamba da ya gabata a Maiduguri.