1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iswap na yin garkuwa da yara 20 a kusa da Chibok

Abdourahamane Hassane
January 21, 2022

Rahotanni daga Jihar Borno da ke a yanki arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayakan kungiyar ISWAP sun kai hari a kauyen Piyemi da ke kusa da Chibok inda suka sace yara 20.

https://p.dw.com/p/45vy1
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Rahotanni daga Jihar Borno da ke a yanki arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayakan kungiyar ISWAP sun kai hari a kauyen Piyemi da ke kusa da Chibok inda suka kashe mutane biyu kana suka yi awan gaba da 'yan mata 13 da samari bakwai. Masu aiko da rahotannin sun ce mayakan na ISWAP sanye da kakin soji sun afkawa kauyen a jiya Alhamis inda suka rika yin harbe-harbe a kan mai uwa da wabi  tare da kwasar ganima a kantina da kuma kona gidaje. Rahotanin sun ce bayan harin Alhamis(20-01-22) sun sake komawa a kauyen a ranar Jumma'a inda suka kona rabin garin a ciki har da ginin coci daya da kuma motoci sama da goma a hare-haren da suka dauki tsawon sa'oi uku.