1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ISWAP da sauran rina a kaba

November 15, 2021

A yayin da mahukuntan Najeriya ke fadin suna yin galaba a cikin yaki da ta'addanci, Kungiyar ISWAP na kokarin sake dawo da kai hare-hare.

https://p.dw.com/p/4325s
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Ya zuwa yanzu dai jami'an tsaron Najeriyar sun ce sun kashe manyan jiga-jigai na kungiyoyin na 'yan ta'adda irinsu Abubakar Shekau da ke zaman shugaba na farkon fari, da ma shi kansa Abu Musab Albarnawi da ya kwaci shugabancin daga baya. Ko bayan mika wuyar yayan kungiyar kusan 15000 da Abujar ta tabbatar a wani abun da ta ce na nuna alamun farkon karshen rikicin na shekaru 12.

Duk da ikirarin da gwamnatin Najeriya take yi na kawo karshen ISWAP, kungiyar na ci gaba da kai hare-hare

Nigeria ISWAP Anschlag in Borno
Hoto: AFP/A. Marte

To sai dai kuma a wani abun da ke kama da da shi mai rai guda tara, masu ta'addar na kuma tashi daga kabari tare da tafka ta'addanci walau ga jami'an tsaron Najeriyar ko kuma raguwa na mazauna na gari. Ko a farkon wannan mako dai ra'ayi ya bambanta a tsakanin jami'an tsaron tarrayar Najeriyar da ke fadin sun yi asarar wasu hafsoshin soja hudu da kuma 'yan kungiyar da suka ce sun hallaka 17 a garin Askira Uba da ke sashen kudancin Jihar ta Borno da ke zaman tungar rikicin. Ana dai kallon rikida ta kungiyar da majiyoyi suka ce ta mamaye arewacin jihar a halin yanzu kuma ta yi nisa wajen kwanatr da hankula na mazauna yankin a wani sabon salon na dauke hankalin mazauna yankin a fadar Senata Ali Ndume da ke zaman dan majalisar dattawa daga Jihar ta Borno kuma shugaban kwamitin kula da sojan kasa na majalasar dattawa ta kasar.