1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari tashar jirgin ruwan Siriya

December 28, 2021

Rahotanni daga Siriya na cewa Isra'ila ta kai wani hari ta sama a tashar jiragen ruwan kasar dake yankin Latakia, harin da ke zama na biyu da aka kai tashar a wannan watan.

https://p.dw.com/p/44tGc
Syria Israel
Hoto: SANA/AP/picture alliance

Rahotanni na nuni da cewa Isra'ilar ta kaddamar da harin ne da makami mai linzami daga tekun Bahar Rum. Harin dai ya haifar da tashin gobara da kuma lalacewar wasu kayan aiki.

Ko a ranar 7 watan Disambar nan Isra'ilar ta kai hari kan wani jirgin ruwan Iran a Latakia, sai dai kuma ba a sami asarar rayuka ba.

Tun bayan barkewar yakin basasa a Siriya a shekarar 2011 ne Isra'ila ta ke kaddamar da hare-hare ta sama ga makwafciyarta mai fama da rikici, mafi akasari kan dakarun gwamnati da dakarun kawancen Iran da kuma mayakan Hizbullah.